Episode's summary
Shirin Ilimi hasken rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali, ya yi duba ne kan makomar da yarinya mace ke da ita idan aka hanata taɓa alƙalami, aka kuma bata kwanon tallace-tallace a yankunan karkara, yayin da a dai dai wannan lokaci da ake fuskantar matsin tattalin arziki, fargabar tsaro da wasu tsoffin al'adun gargajiya na ci gaba da raba 'yan mata samun damar shiga ajujuwan karatu, musamman a Arewacin Najeriya da yankin tafkin Chadi. Shin wace rawa muryoyin dake cikin al'umma za su taka wajen ceto goben yarinya mace? Cikin mintuna goma na wannan shiri na musamman, za mu ji muryoyin da ke fuskantar wannan kalubale da kuma masu neman mafita. Mu fara da duba ainihin abin da ke faruwa a cikin makarantun karkara, inda karancin dalibai mata ke dada fitowa fili musamman idan sun fita daga firamare sun shiga sakandare. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

Episodes
Yadda maye gurbin makaranta da yawon talla ke kassara rayuwar mata a Najeriya
ListenedShirin Ilimi hasken rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali, ya yi duba ne kan makomar da yarinya mace ke da ita idan aka hanata taɓa alƙalami, aka kuma bata kwanon tallace-tallace a yankunan karkara, yayin da a dai dai wannan lokaci da ake fuskantar matsin tattalin arziki, fargabar tsaro da wasu tsoffin al'adun gargajiya na ci gaba da raba 'yan mata samun damar shiga ajujuwan karatu, musamman a Arewacin Najeriya da yankin tafkin Chadi. Shin wace rawa muryoyin dake cikin al'umma za su taka wajen ceto goben yarinya mace? Cikin mintuna goma na wannan shiri na musamman, za mu ji muryoyin da ke fuskantar wannan kalubale da kuma masu neman mafita. Mu fara da duba ainihin abin da ke faruwa a cikin makarantun karkara, inda karancin dalibai mata ke dada fitowa fili musamman idan sun fita daga firamare sun shiga sakandare. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
Yaɗuwar fasahar AI a harkar koyo da koyarwa
ListenedA wannan makon, shirin namu ya yi duba ne ga guguwar fasahar zamani ta Artificial Intelligence ko kuma AI, da kuma yadda take sauya fasalin yadda ake koyo da koyarwa a makarantunmu. Ko wace makoma ce ke jiran azuzuwanmu na gaba a daidai lokacin da dalibai suka rungumi amfani da manhajoji irin su ChatGPT da Google Gemini? Gudunmowa ko kuma illar da fasahar AI ke da ita ga dalibai na ci gaba da daukar hankalin masana. A yayin da wasu ke kallon ta a matsayin wata babbar dama ta samun ilimi cikin sauki, wasu kuwa na fargabar cewa za ta sanya dalibai lalaci ko kuma ta maye gurbin malamai gaba daya.
Matakin sallamar shugabannin makarantu sama da ɗari 4 a Nijar ya haifar da cece-kuce
ListenedShirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon ya maida hankali ne kan matakin sallamar shugabannin makarantu sama da ɗari 4 da gwamnatin Nijar tayi, bayan da ɗaliban makarantun da suke jagoranta na firamari da kuma sakandare suka gaza samun makin da ake buƙata, lamarin da ya sanya ɗiga ayar tambaya kan ko wannan mataki zai haifar da ɗa mai ido ga ɓangaren ilimin ƙasar. Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Shamsiyya Haruna............
Yadda ƙarancin malamai ke barazana ga harkar ilimi a yankin Afrika
ListenedShirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon zai kai ku kai tsaye zuwa cikin azuzuwan karatu na yankin Afirka ta Kudu da Sahara, yayin da rahoton baya-bayan nan na hukumar UNESCO ya girgiza duniya, inda ya bayyana cewa ana buƙatar ƙarin malamai miliyan Hamsin nan da shekara ta 2030 domin ceto ilimin duniya. Amma abin mamaki da kuma ban tsoro shi ne; kusan miliyan 15 na waɗannan malamai, a nan yankinmu na Afirka ake buƙatarsu. Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Shamsiyya Haruna............
Yadda ambaliyar ta kassara makarantu da dama a arewacin Najeriya
ListenedShirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon ya duba halin da makarantu ke ciki ne a Tarayyar Najeriya sakamakon fuskantar matsalar ambaliyar ruwa a sassa daban daban na ƙasar.